Sabon hari yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da 100 a Benue

0
88

Aƙalla mutane 100 ake fargabar sun mutu sakamakon wani mummunan hari da wasu ‘yan bindiga suka kai wa al’ummar Yelewata da ke ƙaramar hukumar Guma a Jihar Benue.

Harin ya faru ne da safiyar Asabar, inda maharan suka mamaye garin da misalin ƙarfe goma sha biyu na dare, sannan suka yi kaca-kaca da rayuka da dukiyoyi na tsawon sa’o’i fiye da biyu, ba tare da jami’an tsaro sun kawo ɗauki ba.

A wani harin daban da ya faru a garin Daudu, wani ƙauye da ke cikin ƙaramar ta hukumar Guma, an kashe sojoji biyu.

Garin na Daudu yana da tazarar tafiya ta kusan minti 20 daga Makurdi, babban birnin jihar.

Harin na Yelewata shi ne na uku a cikin mako guda da aka kai garin, wanda ke kan iyakar Benue da Nasarawa. 

Shugaban ƙaramar hukumar Guma, Maurice Orwough, bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba har zuwa lokacin da ake rubuta wannan rahoto,don samun ƙarin bayani akan lamarin.

Mai bai wa Gwamnan Jihar Benue shawara kan harkokin tsaro da cikin gida, Chief Joseph Har, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Makurdi, sai dai ya ce, ba zai iya bayar da cikakken bayani ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here