Shugaban ƙasar Isra’ila, Isaac Herzog, ya bayyana wannan safiyar a matsayin lokaci mai cike da baƙin ciki da wahala, a sakon da ya wallafa a shafinsa na X, a lokacin da ƙasar ta fuskanci hare-haren da Iran ta kai cikin tsakiyar Isra’ila da kuma wasu sassa na arewacin kasar.
Herzog ya bayyana hare-haren na Iran da cewa “munana ne ƙwarai”, inda ya ce sun yi sanadiyyar mutuwa da raunata mutane da dama, wanda suka ƙunshi Yahudawa da Larabawa, ‘yan ƙasar Isra’ila da ma baƙi ‘yan ƙetare ciki har da yara da tsofaffi, mata da maza.
Zuciyata na tare da iyalan da suka rasa masoyansu. Ina addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata, da kuma fatan a gano waɗanda aka nema aka rasa. Za mu yi makoki tare, kuma za mu fuskanci wannan ƙalubale tare,” in ji Herzog.