Ba da amincewar iyayena na auri mata ta ba—Atiku Abubakar

0
117

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana yadda ya bijirewa umarnin iyayensa don ya auri matarsa ta fari, Hajia Titi Atiku Abubakar, fiye da shekaru hamsin da suka wuce, inda ya bayyana ta a matsayin babban alkairi a rayuwarsa da kuma danginsu.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin bikin zagayowar ranar haihuwar Hajia Titi na cika shekara 75 da aka gudanar a Abuja a ranar Asabar. Bikin ya samu halartar abokai na kusa, dangi da kuma abokan siyasar Najeriya.

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku ya yaba da hakuri da goyon bayan matarsa na tsawon shekaru da dama.

“A lokacin cikar abar kauna ta shekara 75, ina alfahari da cewa ban taɓa yin nadamar auren wannan mata ba. Mun yi aure cikin ƙarfin hali ba tare da amincewar iyayenmu ba kuma tare da abokai biyu kacal aka daura auren,” in ji Atiku.

“Yau, bayan fiye da shekaru 50, Titi ta zama albarka mai yawa a gare Ni, ina gode mata bisa juriya da hakuri, musamman da kuskurena. Ban ma tuna yadda muka fara kiran juna ‘Mummy’ da ‘Daddy’ ba, amma ina matuƙar godiya da wannan tafiya,” ya ƙara da cewa.

Atiku ya shawarci ma’aurata su riƙa hakuri da juna a zaman aure, yana cewa “hakuri ɗabi’a ce da ba za ku taɓa nadama ba. Ina ƙarfafa ma’aurata da su yi hakuri da juna.”

Hajia Titi, wadda aka haifa da suna Titilayo Albert, asalinta daga ƙabilar Yarbawa ce Kirista daga garin Ilesa da ke jihar Osun. An haife ta kuma ta girma a Legas, inda ta halarci makarantar firamare ta Lafiaji, sannan ta ci gaba da karatu a St. Mary’s, Iwo, inda ta kammala sakandire a 1969.

Ta auri Atiku a shekarar 1971 lokacin yana matashin jami’in kwastam. Daga baya ta karanci ilimi a Kwalejin Kimiyya ta Kaduna (Kaduna Polytechnic), inda ta kuma yi aikin koyarwa. Hajia Titi na iya magana da Ingilishi, Yarbanci da Hausa. Ta sauya addininta daga Kiristanci zuwa Musulunci bayan auren su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here