A’lummar Katsina sunyi sulhu da ɗan bindiga Ado Aleru

0
32

Wasu al’ummar garin Bicci da ke ƙaramar hukumar Danmusa, jihar Katsina, sun cimma matsaya ta zaman lafiya da wasu manyan shugabannin ƴan bindiga da suka addabi yankin.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Katsina, Dakta Nasiru Mu’azu, ya bayyana cewa shahararrun shugabannin ƴan bindigar da aka tattauna da su sun haɗa da Ado Aleru, Kamilu Buzaru, Dogo Nahali, Wada Jargaba, Dahiru Buzu da Nagoggo.

Lamarin ya faru ne bayan wasu daga cikin ƴan bindigar sun nemi sulhu, duk da matsayar gwamnatin Katsina da ta sha nanata cewa ba za ta sasanta da ƴan bindiga ba. Sai dai kwamishinan ya ce buƙatar zaman lafiar ta fito ne daga ɓangaren ƴan bindigar, lamarin da ya sa aka ba su dama domin rage tashin hankali a yankin.

Ƴan bindigar sun sha alwashin ajiye makamansu da sako waɗanda suka yi garkuwa da su.

Tun a baya, an samu irin wannan zaman sulhu a wasu yankuna kamar Jibia da Batsari, inda hakan ya taimaka wajen rage hare-hare.

A wani ci gaba kuwa, rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta ce ta ceto mutum 73 da aka yi garkuwa da su tare da cafke mutum 75 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban. An kuma ƙwato bindigogi, harsasai, babura da shanu 174 da ake zargin an sace su.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here