Majalisun dokokin ƙasa sun ƙara ayyukan Naira triliyan 10.96 a kasafin kuɗin Najeriya

0
96

Wasu kungiyoyin farar hula da suka haɗa da (SERAP) da (CACOL) sun soki Majalisun dokokin Ƙasa bisa zargin ƙara wasu ayyuka da suka kai naira tiriliyan 10.96 a cikin kasafin kuɗin Najeriya daga shekarar 2021 zuwa 2025.

Kungiyoyin sun bayyana hakan a matsayin wuce gona da iri a wajen amfani da ikon da doka ta ba Majalisar, suna mai kiran hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da su gaggauta bincike kan wannan batu.

A cewar wata kungiya mai bincike a fannin fasahar ɗemokuraɗiyya, wato BudgIT, a wani rahoto da ta fitar a ranar Alhamis, Majalisar Ƙasa ta ƙara jimillar ayyuka 30,632 na mazabu a cikin kasafin kuɗi na shekarun 2021, 2022, 2024 da 2025.

BudgIT ta bayyana a shafinta na X cewa, shekarar 2021, an ƙara ayyuka 5,601 da suka kai naira biliyan 913.15

A 2022, an ƙara ayyuka 6,462 da suka kai naira biliyan 910.37

A cikin kasafin 2024, an saka ayyuka 7,447 masu darajar naira tiriliyan 2.24

A shekarar 2025, an ƙara ayyuka 11,122 da suka kai naira tiriliyan 6.9

Rahoton ya kara da cewa a cikin kasafin 2025 kaɗai akwai ayyuka 3,573 da suka kai naira biliyan 653.19 da aka tanada a mazabun ‘yan majalisar wakilai, sannan akwai ayyuka 1,972 da suka kai naira biliyan 444.04 da aka ware wa mazabun Sanatoci.

Daga cikin ayyukan da majalisun suka saka a kasafin 2025 akwai, aikin sanya fitilun titi da suka kai naira biliyan 393.29, sai rijiyoyin burtsatse da darajarsu ta kai naira biliyan 114.53

Ayyukan da suka shafi fasahar sadarwa (ICT) – naira biliyan 505.79

Gini da gyaran zaurukan taron al’umma naira biliyan 17.23

Ayyukan da suka shafi ilimi naira biliyan 179.69

Sauran ayyukan sun haɗa da;

Fannin lafiya naira biliyan 420.09

Tallafa wa sarakunan gargajiya naira biliyan 6.74

Gine-ginen hanya da gyara su naira tiriliyan 1.44

Siyan motocin jami’an tsaro naira biliyan 11.7

Kungiyoyin sun yi kira da a dakile wannan dabi’a da ke lalata tsari da gaskiya a cikin kasafin kuɗi, suna mai nuna damuwa da yadda ake ci gaba da amfani da kasafin kuɗi wajen biyan buƙatun siyasa maimakon amfanin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here