Gwamnatin tarayya ta soke umarnin yin Azumi don samar da abinci a Najeriya

0
113

Ma’aikatar aikin gona da samarwa ƙasa isasshen abinci ta soke umarnin da ta bayar a baya na gudanar da zaman addu’a da azumi domin neman jagorancin Allah da nasara wajen tallafa wa gwamnatin tarayya wajen samun abinci ga al’ummar Najeriya.

Wannan matakin ya biyo bayan suka da ce-ce-ku-ce daga al’umma dangane da shirin ma’aikatar na dogaro da addu’a don magance matsalolin karancin abinci da tsadar rayuwa da ke addabar ‘yan kasa.

Wasu bayanan da suka fita fili, da ke dauke da kwanan wata 11 ga Yuni, da kuma sanya hannun Daraktar Kula da Ma’aikata na ma’aikatar Adedayo Modupe O., sun gayyaci manyan ma’aikata da suka hada da daraktoci, mataimakan daraktoci, da jami’an kula da harkar samar da kayayyaki, zuwa zaman addu’a na kowane mako da za a gudanar a babban ofishin ma’aikatar da ke Abuja.

An yi wa shirin suna da taken: “Shiga Tsakani Allah don Kariya da Cigaban Kasa”, inda aka tsara gudanar da zaman a ranakun 16, 23, da 30 ga Yuni. A cikin sanarwar, dukkan ma’aikata an umurce su da su yi azumi tare da halartar zaman addu’ar.

Sai dai, cikin wata sabuwar sanarwa daga daraktar da ta fitar da umarnin farko, ta bayyana cewa an dage zaman addu’ar har zuwa wani lokaci da ba a kayyade ba, sannan ba a bayyana dalilin dagewar ba a hukumance.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here