Ba zamu saurarawa Isra’ila ba—Ayatollah

0
81

Jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya bayyana cewa Isra’ila ce ta fara tayar da tarzomar yaki, kuma Iran ba za ta yi shiru ba dangane da hare-haren da ake kai mata.

A cewarsa bai kamata su yi tunanin za su kai farmaki kuma komai ya wuce haka ba. Su ne suka fara, su ne suka kunna wutar yaki, kuma ba za mu bar su haka nan ba.

Kalaman na Khamenei na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Ɗinkin Duniya ke gudanar da taron gaggawa na kwamitin tsaro, domin tattauna rikicin da ke ci gaba da ƙamari tsakanin ƙasashen biyu.

Jakadan Iran a wannan taro ya ce hare-haren da Isra’ila ta kai ya yi sanadin mutuwar mutane 78 mafi yawan su fararen hula tare da raunata wasu da dama. Ya ce farmakin ya afka kan cibiyoyin soja da na nukiliyar Iran, sannan ya shafi yankunan fararen hula.

A nata bangaren, Isra’ila ta bayyana cewa farmakin da ta kai wani mataki ne na hana Iran mallakar makaman nukiliya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here