Mutum takwas daga gida guda sun rasa rayukansu, yayin da wasu biyu ke karbar magani a asibiti sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a Barakallahu, kan hanyar Kaduna zuwa Zariya, da yammacin Litinin a lokacin bukukuwan Babbar Sallah.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon wata mota kirar GLK mai gudu wuce kima, wadda ta kwace daga hannun direbinta wani yaro da ake zargin dan wani fitaccen dan siyasa ne.
Motar ta afka kan wasu mutane da ke tsaye a gefen hanya bayan dawowarsu daga yawon sallah.
Malam Jamilu Usman Maiyadi, mahaifin wasu daga cikin mamatan, ya ce ya rasa matarsa da ’ya’yansa biyu, da wasu ’yan uwa guda biyar duk a rana guda.
Ya bayyana cewa mutanen na tsaye ne suna jiran motar haya lokacin da hatsarin ya auku.
Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da faruwar lamarin, tana danganta shi da gudu fiye da kima da kuma kwacewar mota a kan hanya mai danshi bayan saukar ruwan sama.
Hukumar ta ce ta mika al’amarin ga rundunar ’yan sanda domin ci gaba da bincike.