Isra’ila ta kashe manyan jami’an ƙasar Iran a wani harin data kai mata

0
53

Aƙalla masana ilimin haɗa makamin nukiliya shida ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kaiwa Iran a ranar Juma’a, kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran suka ruwaito.

Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya bayyana sunayen waɗanda suka mutu, ciki har da Mohammad Mehdi Tehranchi, wanda ya kasance shugaban Jami’ar Azad ta Islama a Iran.

Hakanan, rahoton ya tabbatar da mutuwar Fereydoun Abbasi, tsohon shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, yana daga cikin waɗanda suka mutu a harin.

Harin na ranar Juma’a ya afka akan wurare da dama a fadin ƙasar, ciki har da gidajen zama a birnin Tehran da kuma wani muhimmin wurin sarrafa makamashin nukiliya da ke tsakiyar Iran.

Rahotanni sun ce shugaban rundunar ’Yan Sanda na Juyin Juya Hali na Iran, Hossein Salami, da kuma Mohammad Bagheri, babban hafsan hafsoshin rundunonin sojin Iran, suma sun mutu a harin da Isra’ila ta kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here