Ƙungiyar cigaban garin Rimin Zakara ta ƙaryata labarin yi musu rusau

0
80

Kungiyar cigaban garin Rimin Zakara, ta ƙaryata labarin cewa an zo domin yin sabon rusau a gidajen su, tare da korar sakataren ta Mustapha Aliyu, da akace shine ya fitar da labarin rusau din bisa ra’ayin kansa da kansa.

Babban limamin garin Malam Rabi’u Zakariyya, yace babu gaskiya a labarin da tsohon sakataren kungiyar cigaban garin Rimin Zakara ya sanar inda suka ce babu wani labarin rusau da suka samu 

Shima shugaban matasan garin Magaji

Idris, yace suna zaune cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ko fargaba ba.

Malam Shua’aibu Mahammmad ɗaya daga cikin shugabanin garin yace waccen magana babu ita Kuma masu fadin hakan basa kishin garin don haka basa goyon bayan wadancan kalamai kuma suna tare da duk abinda gwamnnatin jihar Kano tazo dashi 

Alhaji Baba Habu Mika’ilu, rimin Zakara, wanda shine shugaban Kungiyar cigaban garin, yace wanna Jan fenti da aka gani a jikin gidaje anyi ne don kidaya gidajen yankin don samar da cigaban garin kamar yadda a baya gwamnan kano ya samar da wutar lantarki a garin, kuma basa goyon bayan faruwar wani abu mara dadi ya faru a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here