Kamfanin mai na ƙasa NNPC, ya bayyana samun ribar Naira biliyan 748 bayan cire haraji a watan Afrilu na shekarar 2025.
Wannan na kunshe cikin rahoton kamfanin na wata-wata mai inda kamfanin ya bayyana cewa ya samu kudaden shiga da suka kai Naira tiriliyan 5.89 a cikin watan.
Kamfanin ya kara da cewa, daga watan Janairu zuwa Maris 2025, ya biya Naira tiriliyan 4.22 a matsayin kudaden da dokar ƙasa ta wajabta masa.
“Dukkan wadannan alkaluma na kudi ba a kammala tantance su ba, kuma ba a gudanar da binciken lissafi na ƙarshe a kansu ba,” in ji kamfanin.
A fannin samar da mai, NNPC ya bayyana cewa ana fitar da gangar danyen mai guda miliyan 1.60 a kowace rana a watan Afrilu. Haka kuma, ana samar da gas.