Mahaifiya ta kashe ƴarta akan ɓatan Naira 100

0
133
Kaduna

Wani mummunan lamari mai tayar da hankali ya faru a garin Zariya, dake Jihar Kaduna, bayan da wata mata mai suna Khadija ta zargi ‘yarta Fadila mai shekaru 11 da sata, inda ake zargin hakan yasa ta buge yarinyar har ta mutu saboda ɓatan Naira 100.

Lamarin ya faru a yammacin ranar Asabar a unguwar Tukur, kafin sallar Magariba. 

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa Khadija ta zargi Fadila da satar kudin da aka bata lokacin bikin Sallah. 

A cikin fushi, ta dauki wani abu ta dinga dukan yarinyar, lamarin da ya yi sanadin mutuwarta.

Wasu mazauna unguwar sun bayyana cewa Khadija ta saba dukan Fadila akan kananan dalilai, musamman game da sana’ar tallace-tallacen da yarinyar ke yi a titi.

Da yake magana da manema labarai, mahaifin marigayiyar, Malam Mustapha Musa, ya ce yana wajen aiki lokacin da abin ya faru. Ya ce ya dawo gida ne kawai ya iske labarin rasuwar ‘yarsa, inda ya kara da cewa tuni ya dauki gawarta zuwa garinsu a Jihar Kano domin jana’iza.

Khadija ta amsa laifin dukan Fadila, amma ta ce ba da niyyar kashe ta ta yi ba, tana danganta abin da ya faru da “tsananin damuwa” da ta shiga a lokacin.

Jami’an tsaro daga kungiyar sa-kai na yankin ne suka fara daukar mataki kafin daga bisani su mika lamarin ga ‘yan sanda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here