An tsallake rijiya da baya a jihar Kano a ranar Laraba, bayan wata babbar tanka dauke da man fetur ta kwace yayin da take ƙoƙarin shiga wani gidan mai da ke kan titin BUK-Gwarzo, lamarin da ya haifar da firgici a tsakanin mazauna yankin, da masu wucewa.
Lamarin ya faru ne a kusa da mahaɗar zuwa ofishin hukumar masu hidimar ƙasa NYSC dake Kano, inda tankar da ke cike da man fetur ta kusa yin hatsari, lamarin da ya tayar da hankulan jama’a saboda fargabar gobara ko fashewar tankar.
Hukumomin bada agajin gaggawa, hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC), Hukumar kashe gobara ta Tarayya, Red Cross da Hukumar KAROTA sun isa wurin cikin gaggawa domin dakile lamarin.
Yin aiki akan lokaci da hadin kai tsakanin hukumomin ya taimaka wajen hana aukuwar mummunar gobara.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar yaba da jarumtaka da ƙwarewar jami’an da suka halarci wajen.
Ya ce, jarumtaka da saurin daukar matakin jami’an ya hana aukuwar bala’i, tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi da kuma dawo da yanayin zirga-zirga yadda ya kamata abun yabawa ne.
Gwamnan ya jinjina wa hadin kai da aiki tare da hukumomin, yana mai cewa wannan hadin gwiwa da gaggawar daukar mataki su ne suka taka muhimmiyar rawa wajen dakile hatsarin.
Haka kuma, ya yi kira ga direbobin tankoki da masu gidajen mai da su rika bin ƙa’idojin tsaro sosai yayin saukewa da ɗaukar mai, domin guje wa faruwar hadari a gaba.
Gwamna Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyi, yana mai tabbatar da cewa za su ci gaba da daukar matakan gaggawa da karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomin domin kare al’umma a faɗin Jihar Kano.