Bayan wani taron da iyalan marigayi Sarkin Kano, Khalifa Sir Muhammadu Sanusi, suka gudanar sun nesanta kansu daga halayen da suka kira na rashin ɗa’a da rashin kunya da suka danganta sarkin Kano na 16, Sunusi Lamido Sunusi, dasu.
Cikin wata sanarwar da Alhaji Isa Sunusi (Pilot) ya fitar, iyalan sun bayyana damuwarsu kan yadda suka ce Muhammadu Sunusi II, ke tafiyar da harkokinsa cikin yanayi da ke kara janyo musu tozarci da kunyata su a idon duniya.
Wannan ne ya sa suka gudanar da wani taro a lokacin bikin Sallah domin daukar muhimman matakai da nufin kare mutuncin sunan iyalinsu, inji sanarwar.
Daga cikin matakan da suka ɗauka akwai;
- Fitar da kansu daga zarge-zargen tada husuma da cin mutunci da aka ce tawagar Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sunusi, sun yi wa dattijon Kano, Alhaji Aminu Dantata, a yayin wani jerin gwanon sallah da ya gudanar duk da takunkumin da ‘yan sanda da kotu suka sanya, inda aka zargi tawagar sa da harba bindigogin baka a gidan Dantata da nufin hayaƙin zai cutar da shi. Iyalan sun bayyana wannan a matsayin abin ƙyama da rashin hankali, kuma sun nesanta kansu daga wannan lamari.
- Nesanta kansu daga kiyayya da adawa da wasu daga cikin ‘ya’yan gidan Sarki Ado Bayero, inda suka bayyana cewa Sarkin na 16 ba ya wakiltarsu a irin wannan dabi’a, kuma yana aikata hakan ne a matsayinsa na mutum ɗaya.
- Shawarwarin da suka yanke ya shafi sunan mahaifinsu, inda suka bayyana cewa ba sa goyon bayan yadda sarki Muhammadu Sunusi ke ci gaba da amfani da sunan marigayi Sir Muhammadu Sanusi, kasancewar yana jawo masa abun kunya. Sun shawarce shi da ya koma amfani da sunan mahaifinsa na gaskiya, wato Sunusi Aminu.
A ƙarshe, iyalan sun yi addu’a domin ci gaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Kano da Najeriya gaba ɗaya.