Za’a shafe kwanaki 4 babu Lantarki a wasu jihohin Arewa—TCN

0
266
wutar lantarki

Kamfanin rarraba wutar lantarki na ƙasa (TCN) ya sanar da kamfanonin rarraba wuta (DisCos) da ke aiki a jihohin Arewa Maso Gabas guda shida cewa za a samu katsewar wutar lantarki a yankin, inda wasu wurare za su fuskanci karancin wutar lantarki sosai.

Cikin wata wasika da TCN ua aika wa daya daga cikin kamfanonin rarraba wutar, wacce Injiniya J.O Joseph, Manajan Ayyuka na Yankin Bauchi ya sanya wa hannu, an bayyana cewa dalilin katsewar wutar ya samo asali ne daga aikin gina sabbin turakun wuta na “Turn-In” da “Turn-Out” na 330kV a sabuwar tashar rarraba wuta ta Bauchi.

Sanarwar ta bayyana cewa za a dakatar da samar da wutar lantarki daga ƙarfe 10:00 na safe ranar Talata, 10 ga Yuni, zuwa ƙarfe 5:00 na yamma ranar Asabar, 14 ga Yuni, 2025, sannan wannan dakatarwar za ta shafi layin wutar 132kV na Jos-Bauchi-Gombe.

Bayan sake duba jadawalin aikin kamfanin da ke aikin, an bayyana cewa layin wutar Jos-Gombe za a rufe shi na tsawon wancan lokacin da aka ambata domin ba da damar aikin sanya sabbin turakun wuta a sabuwar tashar Bauchi.

 Wannan yana nufin cewa za a katse wutar lantarki a Damaturu, Molai, Yola da Jalingo, yayin da tashoshin Gombe da Biu za su samu wuta daga tashar samar da wuta ta ruwa ta Dadin Kowa, sannan tashar Baga Road za ta samu wutar daga MEPP.

TCN yace wannan sanarwar ta rushe duk wata sanarwa da aka fitar a baya dangane da aikin.

A cikin wata sanarwa da kamfanin rarraba lantarki na Yola ya fitar, ya tabbatar da wannan ci gaba, inda ya ce katsewar wutar lantarki za ta shafi wasu sassan jihohin Adamawa, Borno, Taraba da Yobe daga ƙarfe 10:00 na safe ranar Talata, 10 ga Yuni zuwa ƙarfe 5:00 na yamma ranar Asabar, 14 ga Yuni, 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here