Za’a samu ruwan sama mai ƙarfi tsawon kwanaki 3 a Kano da wasu jihohin Arewa—NIMET

0
295

Hukumar dake kula da hasashen yanayi ta ƙasa (NiMet) ta yi hasashen cewa za a fuskanci ruwan sama mai haɗe da guguwa daga ranar Laraba zuwa Juma’a a sassan daban-daban na ƙasar nan.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Talata a Abuja, ta bayyana cewa ana sa ran za a samu guguwa da ruwan sama tun da safe a wasu sassan jihohin Taraba, Kaduna da Adamawa a ranar Laraba.

NiMet ta kuma ce daga bisani a ranar, ana sa ran guguwa da ruwan sama za su ci gaba a wasu sassan jihohin Kebbi, Taraba, Zamfara, Katsina, Kaduna, Kano, Sokoto, Gombe da Bauchi.

A yankin Arewa ta tsakiya kuwa, hukumar ta yi hasashen samun guguwa tun da safe a sassan jihohin Benue, Kwara, Neja, Abuja da Nasarawa.

Daga bisani da rana, ana sa ran guguwa tare da ruwan sama a wasu sassan Abuja, Neja, Nasarawa, Kwara, Kogi da Filato.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here