Wani mummunan rikicin cikin gida a kauyen Chirokusko da ke ƙaramar hukumar Tarmuwa, Jihar Yobe, ya yi sanadin mutuwar wani yaro mai shekara 17, Abdulra’uf Abdullahi, wanda ake zargin mahaifinsa ne ya kashe shi.
Lamarin ya faru a daren Litinin, 9 ga Yuni, da misalin ƙarfe 10, kamar yadda Zagazola Makama, mai sharhi akan harkokin tsaro ya tabbatar.
A cewar wasu rahotanni, mahaifin ya cakawa yaro wuka a ƙirji yayin wata mahawara mai zafi tsakanin su, wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar matashin.
Ko da yake ba a tabbatar da musabbabin rigimar ba, sai dai jami’an ‘yan sanda sun hanzarta kai dauki, inda suka garzaya da Abdulra’uf zuwa Asibitin Gwamnati na Babbangida. Amma likitoci sun tabbatar da mutuwarsa a lokacin da suka isa asibitin.
Bayan faruwar lamarin, wanda ake zargi wato mahaifin ya tsere daga wurin da abin ya faru.
Zuwa yanzu rundunar ‘yan sanda ta fara farautar sa domin kama shi da tabbatar da cewa ya fuskanci hukunci.