Jami’an rundunar ‘yan sanda ta musamman mai kula da laifukan damfara (SFU) sun gurfanar da wani Ba’indiye tare da wasu mutum 12 ‘yan Najeriya a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos, bisa zarginsu da karkatar da man dizel da kudinsa ya kai naira biliyan 4 mallakin kamfanin Dangote.
An gurfanar da wadanda ake zargin a gaban Mai Shari’a Deinde Dipeolu, inda ake tuhumarsu da laifuka 16 da suka shafi hada baki wajen aikata laifi, karkatar da dizel ba bisa ƙa’ida ba, da kuma karɓar kuɗaɗe ta l haramtacciyar hanya.
Lauyan masu ƙara, M.Y. Bello, ya bayyana wa kotu cewa wadanda ake tuhuma sun hada da ma’aikatan kamfanin Dangote da wasu ma’aikata daga kamfanonin jigilar fetur irin su Arigen Integrated Ltd, Obat Ltd, Amaiden Energy Ltd, Regal Gate Ltd, Alkham Ltd, Prestige Ltd da Opetrus Global Ltd.
An bayyana cewa dizel ɗin da aka karkatar ya kai lita miliyan 1.53, wanda aka kiyasta kudinsa a kan naira biliyan 1.53. Ba’indiyen da ake zargi na daga cikin ma’aikatan kamfanonin Regal Gate Ltd, Alkham Ltd da Prestige Ltd, inda ya ke aiki da su bisa kwangila da kamfanin Dangote.
Lauya Bello ya bayyana cewa laifukan sun faru ne tsakanin watan Janairun 2022 zuwa Disamban 2023, kuma sun sabawa dokokin Najeriya akan halatta kudaden haram.
Kotu ta bayar da beli ga wasu daga cikin wadanda ake zargi bisa sharuddan da ba a bayyana ba, yayin da aka daga sauraron shari’ar zuwa ranakun 22 da 23 ga watan Yuli.