Kotun ɗaukaka ƙara tayi watsi da bukatun Akpabio akan Natasha

0
149

Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta yi watsi da wasu bukatu guda biyu da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya shigar, inda ta ci shi tarar Naira 100,000.

Kwamitin alkalai uku na kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Hamman Barka, ya yanke wannan hukunci a ranar 21 ga Mayu, 2025, bayan Akpabio ya janye ƙarar da ya shigar da kansa, kan rikicin dake faruwa tsakanin sa da Sanata Natasha, wadda kwamitin majalisar dattawa ya dakatar kan zargin aikata ba daidai ba.

A wani kwafin hukuncin da jaridar PUNCH ta samu a daren ranar Talata, an bayyana cewa ƙorafe-ƙorafen da aka shigar sun kasance daga ranar 3 da 25 ga Maris, 2025, masu lamba CV/395/M1/2025 da CV/395/M2/2025, inda Akpabio ya kasance mai ƙorafi.

Wadanda ake kai ƙarar sun hada da; Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, Sakataren Majalisar Tarayya, Majalisar Dattawa gaba ɗaya, da Shugaban Kwamitin Dattawa kan Ladabi, da Karɓar Ƙorafe-ƙorafe, Sanata Neda Imasuem.

A cikin ƙarar da ya shigar, Akpabio ya nemi kotu ta;

1. Ba shi damar neman izinin daukaka ƙara daga hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke a ranar 10 ga Maris, 2025, a shari’ar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar da Sakataren Majalisar Tarayya da wasu mutum uku.

2. Ba shi izinin ɗaukaka ƙara akan shari’ar sa da Natasha.

Sai dai kotu ta ce tunda ya janye ƙarar da kansa, babu buƙatar ci gaba da sauraron bukatunsa, kuma ta umarce shi da ya biya tarar Naira 100,000 ga ɓangarorin da aka kai ƙara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here