Kotu ta ɗaure wani mutum shekaru 74 a gidan yari

0
152

 

Wata babbar kotu da ke Ajah, a jihar Lagos, ta yanke wa Chukwudi Okonkwo Goodness, hukuncin daurin shekaru 74 a gidan yari bisa laifin satar Naira miliyan 360 da kuma bayar da takardun cirar kudi a asusun bankin da babu kuɗi a cikin sa.

An gurfanar da Goodness ne a shekarar 2016 bisa tuhuma 33 da hukumar EFCC ta shigar. An ce ya karkatar da kuɗin ne daga wani mutum mai suna Henry Nnadike a Ikeja tsakanin watan Yuni da Yuli, 2015.

Bayan shari’ar da ta ɗauki tsawon shekaru tara, mai shari’a Josephine Oyefeso ta same shi da laifi a kan tuhume-tuhume 32. 

Bayan haka an yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a kan tuhuma ta sata, sannan shekaru biyu-biyu a kowace tuhuma daga cikin sauran tuhume-tuhume da suka shafi bayar da katin cirar kudi a asusun da babu kuɗi a cikin sa.

 Haka zalika, an sake yanke masa hukuncin shekaru bakwai a tuhuma ta ƙarshe.

Kotun ta kuma umarce shi da ya mayar da Naira miliyan 215 ga mamallakan su a cikin kwanaki 30.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here