Bayan gobarar da ta tashi a Kasuwar waya ta Farm Centre, Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kwamiti domin bincikar musabbabin lamarin da kuma tsara hanyoyin tallafawa wadanda abin ya shafa.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya ce kwamitin zai tantance asarar da aka yi, gano dalilin gobarar da kuma bada shawarwari domin hana faruwar hakan nan gaba.
Tuni dai an samar da asusun banki domin karÉ“ar tallafi daga jama’a wanda za’a rabawa waÉ—anda lamarin ya shafa.
Sunan Asusun shine: Farm Centre GSM Market Fire Incidence Support Funds Account
Lambar Asusun: 1310076187
Banki: Zenith Bank
Kwamishinan ma’aikatar ayyuka na Musamman, Alhaji Nasiru Sule Garo, ne. jagoran kwamitin tare da wakilai daga hukumomi daban-daban ciki har da jami’an tsaro da ‘yan kasuwa.
A cewar Kwamishinan yaÉ—a labarai da al’amuran cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, yace za a mika rahoton binciken cikin mako guda, ciki har da jerin wadanda abin ya shafa da shawarwari na tsare-tsaren tsaro.