Wasu yan bindiga da ba’a san ko su waye ba, sun kashe direbobi biyu tare da kone motarsu a mararrabar Ogi dake karamar hukumar Okigwe, ta jihar Imo.
Wakilan kungiyar direbobin manyan motoci ta kasa (NURTW), reshen jihar Imo, sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:30 na safiyar Asabar.
Dahiru Musa, shugaban NURTW na Okigwe, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa sun sanar da jami’an tsaro, ciki har da DPO na karamar hukumar Okigwe, game da wannan lamari.
A yayin da yake bayanin lamarin, shugaban ya ce, “Wasu da ake zargin ‘yan IPOB ne sun toshe hanya sannan suka bude wuta a ranar Asabar.
Yace sun kone motar, wadda ke dauke da gari a cikinta, tare da gawarwakin direbobin.
A cewar shugaban, nan take bayan lamarin, ya sanar da jami’an tsaro ciki har da sojoji da ‘yan sanda.
Ni da ‘yan sandan mun kwashe gawarwakin zuwa asibiti, sannan a ranar Litinin, muka yi sallar jana’iza kuma muka binne su,” in ji shi.
A yayin karin bayani, mai magana da yawun NURTW na Manyan Motoci, filin motoci na Laranto, Jos, Mahmud Jafaru, ya bayyana cewa motar na kan hanyar zuwa Port Harcourt lokacin da lamarin ya faru.
Jafaru ya bayyana sunayen direbobin a matsayin Haruna Muhammad da Adamu Ibrahim.
Ya kara da cewa ana kashe direbobi a kowane lokaci. Sannan direban Arewa, ba shi da nutsuwa har sai ya isa Port Harcourt, kuma gwamnati da jami’an tsaro suna ganin kamar ba su da wani matakin É—auka.
Lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Imo, Henry Okoye, bai amsa ba saboda bai É—aga kiran wayar da akayi masa ba.