Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bar birnin Lagos zuwa Abuja, babban birnin tarayya, bayan shafe mako biyu a can.
Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu, ne ya raka shugaban ƙasar zuwa filin jirgin sama na jihar yau Talata.
Tinubu, ya ziyarci mahaifar tasa kafin bukukuwan Sallah Babba, inda yayi Idi a can tare da wasu jami’an gwamnatin tarayya.