Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ɗaukar sabbin ma’aikata a manyan hukumomin tsaro guda huɗu da ke ƙarƙashin Hukumar Kula da Harkokin Tsaro ta Ƙasa (CDCFIB).
Hukumomin da zasu ɗauki ma’aikatan sun ƙunshi;
Hukumar Gidajen Yari ta Ƙasa (NCS)
Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS)
Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa (FFS)
Hukumar Tsaro ta farin kaya ta Ƙasa (NSCDC)
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za a ɗauki ma’aikata masu yawa kamar haka:
Hukumar Gidajen Yari (NCS): 5,150
Hukumar Shige da Fice (NIS): 10,000
Hukumar Kashe Gobara (FFS): 5,000
Hukumar NSCDC: 10,000
Ma’aikatan Sakatariyar CDCFIB: 209
Za a buɗe shafukan yanar gizo na neman aikin daga ranar Jumma’a, 13 ga Yuni, 2025, kuma za su kasance a buɗe na tsawon mako uku. Gwamnati ta jaddada cewa tsarin ɗaukar aikin zai kasance mai gaskiya, bisa cancanta, kuma ba tare da nuna bambanci ba.
Kakakin CDCFIB ya bayyana cewa wannan mataki yana daga cikin shirye-shiryen Shugaba Tinubu na ƙarfafa tsaro a Najeriya, inganta ayyukan gwamnati, da rage rashin aikin yi tsakanin matasa.
Duk da cewa cikakken jerin ƙa’idodin cancanta za su fito ne lokacin da aka buɗe shafin neman aikin, ana sa ran masu neman aikin za su cika wasu sharudda kamar haka:
Dole ne mutum ya kasance ɗan Najeriya, ya mallaki takardun shaidar karatu da suka dace da mukamin da ake nema, ya cika ka’idojin shekaru da lafiyar jiki, sannan ya kasance bai taɓa aikata laifi ba.
Ana shawartar masu sha’awar aikin su fara shirya takardunsu tun yanzu, sannan su rika bin sahihan hanyoyin gwamnati domin samun sabbin bayanai game da aikin da zarar lokacin ya yi.