Fashewar Bam ta hallaka mutane a Sokoto

0
134

Rundunar ‘yansanda ta jihar Sokoto ta tabbatar da rasuwar mutane 6 sakamakon fashewar wani abu da ake zargin bam ne a ƙauyen Gwabro, dake ƙaramar hukumar Tangaza.

A cewar mai magana da yawun rundunar, Ahmad Rufai, lamarin ya rutsa da mutane da dama, kuma ya faru a lokacin bukukuwan babbar sallah.

Wani Shaidu daga ƙauyen, mai suna Hashimu, ya bayyana cewa lamarin ya faru a ranar Lahadi yayin da matasa ke yawo daga ƙauye zuwa ƙauye domin gaishe-gaishen dangi a lokacin sallah.

Garzali Raka, hadimin shugaban ƙaramar hukumar Tangaza, ya ce an yi jana’izar mamatan bisa tsarin addinin Musulunci.

Majiyoyi daga ƙauyen sun danganta fashewar ga ‘yan ta’addan Lakurawa da suka dade suna addabar yankunan ƙananan hukumomin Tangaza da Gudu.

Mazauna yankin sun yi kira ga hukumomi da su kawo karshen barazanar ‘yan ta’adda a yankunan karkara don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here