Mai taimakawa shugaban ƙasa a harkokin jama’a yayi murabus

0
104
Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu

Aliyu Audu, mai taimaka wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na musamman kan harkokin jama’a, ya ajiye aikinsa a hukumance a yau Litinin.

A cikin wata wasika mai shafi ɗaya da aka sanya wa hannun ranar 8 ga watan Yuni kuma aka miƙa ta hannun Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Audu ya bayyana cewa, “Ina rubuto wannan wasika domin in sanar da ajiye aikina daga wannan matsayi aiki nan take.”

Ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu bisa damar da ya ba shi na yin hidima ga ƙasa ƙarƙashin jagorancinsa.

Haka zalika, Audu ya yabawa tsohon mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, wanda ya ba da shawarar da ta kai ga naɗinsa a ranar 26 ga Agusta, 2023.

Naɗin Aliyu Audu ya samu amincewar Shugaba Tinubu a hukumance a ranar 9 ga Oktoba, 2023.

Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, fadar shugaban ƙasa ba tace komai kan hakan ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here