Alhazai sun Kammala aikin Hajjin wannan shekara

0
73

A ranar Lahadi da ta gabata ne kimanin alhazai miliyan 1.8 suka kammala manyan ayyukan ibadar Hajji na bana a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya, bayan gudanar da jifan shaiɗan a Jamarat da ke Mina.

Ko da yake tsarin ibadar Hajji ya tanadi kwanaki shida, addinin Musulunci ya ba da rangwame ga mahajjata su kammala cikin kwanaki biyar, wanda hakan ne ya sa mafi yawan mahajjatan suka kammala ibadar tasu tun ranar Lahadi.

Sai dai wasu daga cikin mahajjatan na ci gaba da ayyukan hajjin, inda ake sa ran za su kammala a ranar Litinin, ta hanyar gudanar da jifan shaiɗan karo na huɗu wanda ake kira Jamrat, fiye da yadda yawanci suke yi sau uku kacal.

Kafin yanzu mahajjatan sun gabatar da muhimman rukunnan Hajji da suka haɗa da hawan Dutsen Arafa, kwana a Muzdalifah, gudanar da ɗawafi a Harami (Ɗawaful Ifadah), da kuma Sa’ayi tsakanin Safa da Marwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here