Za’a shafe kwanaki 3 ana yin ruwa da iska a Kano da wasu jihohi—NIMET
Hukumar Hasashen Yanayi ta Ƙasa (NiMet) ta bayyana cewa ana sa ran za a samu ruwan sama mai haɗe da guguwa daga ranar Lahadi zuwa Talata a sassan ƙasar nan.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Asabar a Abuja, an bayyana cewa za a fara da guguwar da matsakaicin ruwan sama a wasu sassan jihohin Taraba da Adamawa a safiyar Lahadi.
Da yammacin ranar kuma, ana hasashen guguwa tare da ruwan sama a sassan jihohin Taraba, Adamawa, Katsina, Kano, Zamfara, Kaduna, Jigawa, Borno, Gombe da Bauchi.
A yankin Arewa ta Tsakiya kuwa, ana sa ran za a samu gajimare da sanyin safiya.
Sanarwar tace a yayin da rana ke tasowa kuwa, ana tsammanin samin ruwan sama mai haɗe da guguwa a sassan Birnin Tarayya (FCT), da jihohin Neja, Nasarawa, Kwara, Kogi, Binuwai da Filato.