Saboda haɗin kan Najeriya muka yi yaƙin Basasa—Gowon

0
30

Tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soji Janar Yakubu Gowon, ya bayyana yaƙin basasa na Najeriya da akayi a tsakanin shekarun 1967 zuwa 1970 a matsayin “abu mai wuya da ya zama dole, domin tabbatar da haɗin kan ƙasa, ba domin ramuwar gayya ba.

Da yake jawabi a taron shekara-shekara na ƙungiyar Kiristoci taAnglican Men’s Christian Fellowship, da aka gudanar a Abuja, Gowon ya ce, yace yaƙin ba so bane, amma an ɗauki wannan mataki don kare haɗin kan ƙasa. Ba wai saboda ƙiyayya ba.

Ya bayyana cewa matakin da suka ɗauka na hana Biyafara ballewa daga Najeriya ya samo asali ne daga burin ganin Najeriya ta zauna a matsayin ƙasa ɗaya.

 “Mun dakatar da neman ‘yancin kan Biyafara ba don mu murƙushe mutanenta ba, sai don kare ruhin haɗin kan Najeriya,” in ji shi.

Gowon, wanda a yanzu haka ya kai shekara 91, a duniya ya ambato irin raɗaɗin da yaƙin ya bar masa, ciki har da rasa abokai kamar su Major Arthur Unegbe. Ya kuma jaddada bukatar yafiya, sulhu da girmama juna tsakanin ‘yan Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here