Jarrabawar Computer ba zata magance satar amsa ba—NUT

0
42

Ƙungiyar Malaman Makaranta ta ƙasa (NUT) ta bayyana cewa sauya tsarin gudanar da jarrabawa zuwa computer da hukumar (WAEC) da hukumar  (NECO) za su aiwatar, ba zai kawo ƙarshen satar amsa ba.

Shugaban kungiyar NUT, na ƙasa Audu Amba, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) a ranar Lahadi a Abuja.

Amba ya bayyana hakan a matsayin mayar da martani ga umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar na cewa WAEC da NECO su sauya tsarin jarrabawar su daga ta rubutu zuwa computer kafin shekarar 2026.

Musamman, ana sa ran WAEC za ta fara gudanar da jarabawar Computer daga watan Nuwamba 2025.

Ministan Ilimi, Tunji Alausa, wanda ya sanar da matakin gwamnatin tarayya, akan umarnin ya ce canza tsarin jarabawar WAEC da NECO zuwa computer zai inganta tare da rage satar amsar da ɗalibai keyi a lokacin jarrabawa.

Sai dai Amba ya ce babbar matsalar da ke addabar tsarin ilimi a Najeriya ita ce yadda ake bai wa takardar shaidar kammala karatu fifiko fiye da kwarewa, wanda yace hakan ne ke haifar da matsin lamba da ke sanya dalibai su aikata maguɗi yayin rubuta jarrabawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here