Gwamnatin tarayya ta bayar hutun ranar Dimokuraɗiyya

0
37
Bola Tinubu
Bola Tinubu

 

Gwamnatin tarayya ta bayyana Alhamis mai zuwa a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar dimokuraɗiyya ta shekarar 2025.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta sanya wa hannu a ranar Lahadi.

Ministan ya taya ’yan Najeriya murnar cika shekaru 26 na mulkin farar hula ba tare da tangarda ba, tare da yabawa da ƙoƙari da ƙarfin guiwar al’umma da juriya da ƙwazo da suka nuna a tsawon shekarun.

Sanarwar tace hutun zai kasance a ranar Alhamis 12 ga watan Yuni na shekarar 2025.

Tunji-Ojo ya ƙara da cewa, a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, Najeriya na ci gaba da jajircewa wajen mutunta ƙa’idodin dimokuraɗiyya, inda ra’ayoyin ’yan ƙasa ke taka muhimmiyar rawa wajen tsara siyasa, tattalin arziƙi, zamantakewa da al’adun ƴan ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here