Ya kamata shugaban ƙasa da gwamnoni su koma yin shekaru 6 akan mulki—gwamnan Oyo

0
33

Gwamnan Jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, ya bayyana bukatar a rage wa’adin mulki ga dukkan masu rike da mukaman siyasa a Najeriya zuwa zango ɗaya na shekaru biyar ko shida, maimakon tsarin yanzu na zangon shekaru hudu biyu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, lokacin da wasu manyan musulmai da suka haɗa da limamai, sarakunan gargajiya da ‘yan siyasa suka kai masa ziyara a gidansa da ke Ikolaba, Ibadan, bayan kammala sallar Eid-el-Kabir a filin Idi na Agodi, Ibadan.

Wakilan da suka kai ziyarar sun kasance karkashin jagorancin Mataimakin Gwamna, Barista Abdulraheem Bayo Lawal, inda suka haɗa da Otun Olubadan na Ibadanland, Sanata Rashidi Ladoja, tsohon Mataimakin Gwamna kuma Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Jakada Taofeek Arapaja, tsofaffin mataimakan gwamnoni Barista Hazeem Gbolarumi da Injiniya Hamid Gbadamosi, ɗan Majalisar Tarayya Hon. Abass Adigun Agboworin, da kuma Alhaji Dawodu Makanjuola.

Makinde ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar babban bikin Eid-el-Kabir na shekarar 2025, tare da gode musu bisa addu’o’insu, jajircewarsu da kuma goyon baya mara yankewa da suka ba shi da gwamnatinsa a tsawon shekaru shida da suka gabata.

Ya jaddada cewa zangon mulki guda na shekaru biyar ko shida ya isa gwamnati ta mayar da hankali wajen cika alkawuranta da yi wa al’umma na aiki, inda ya yi kira da a yi garambawul ga kundin tsarin mulkin ƙasa domin tabbatar da hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here