Zamu sauya fasalin rundunar ƴan sandan Najeriya—Tinubu

0
63

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da aniyar gwamnatinsa ta sauya fasalin rundunar ƴan sandan kasar da sauran hukumomin tsaro baki ɗaya.

Shugaban ƙasar ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin tarayya za ta ci gaba da saka samar da wajen don samar da kayan aiki, horarwa, da inganta walwala domin ƙarfafa ƙwarewa da ƙwarin gwiwar jami’an ‘yan sanda.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wani bikin bayar da lambar yabo ga Rundunar  ƴan sandan wanda aka gudanar a birnin tarayya Abuja.

Shugaban kasar ya bayyana haka ta bakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, wanda ya wakilci Tinubu a taron.

Ya ce: “Gwamnatina na da cikakken ƙuduri wajen gyara da sake daidaita harkokin ƴan sandan Najeriya. 

Mun fahimcibcewa aikin ‘yan sanda na buƙatar kayan aiki na zamani, dabarun leƙen asiri na zamani, haɗin gwiwa da al’umma, da kuma horarwa.

Shugaba Tinubu ya taya waɗanda suka samu lambobin yabo na shekarar 2024 murna, tare da yaba musu bisa sadaukarwa da suka nuna yayin aikin su, yana mai ƙarfafa su da kada su yi sakaci da nasarorin da suka cimma.

A nasa jawabin, Sanata Akpabio ya sanar da bayar da gudummawar naira miliyan biyar (₦5m) ga iyalan marigayiya Kwamishinan ‘Yan Sanda mai rikon ƙwarya, Aniedi Cecilia Udoh, wadda aka karrama a matsayin “Jajirtacciyar Jakadiyar Tsaron Al’umma ta Shekara ta 2024” bayan rasuwarta.

Udoh, wadda ta rasu a watan Mayu a lokacin da take bakin aiki, ita ce Kwamandan yanki na Ahoada a Jihar Rivers, wadda aka haifa a Jihar Akwa Ibom.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here