Yajin aikin ma’aikatan lantarki zai janyo rashin wuta a Abuja da wasu jihohi 3

0
70

Ana fargabar samun katsewar wutar lantarki a birnin tarayya Abuja, sakamakon shirin shiga yajin aiki da ma’aikatan wutar lantarki ke yi, waɗanda ke ƙarƙashin ƙungiyoyin (NUEE) da kuma (SSAEAC).

Ƙungiyoyin biyu, waɗanda ke aiki tare da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), sun bayyana cewa yajin aikin aikin da suke shirin shiga yana da nasaba da rashin aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma bayan dakatar da wani yajin aiki a watan Nuwamba na shekarar 2024.

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa kamfanin AEDC ce ke da alhakin rarraba wutar lantarki a Abuja, Jihar Neja, Nasarawa da kuma Kogi.

A lokacin yajin aikin da aka dakatar a watan Nuwamba, ma’aikatan AEDC sun yi zanga-zanga a harabar hedikwatar kamfanin, kafin a cimma matsaya da ta kai ga dakatar da yajin aikin.

A cikin wasiƙun da kowace ƙungiya ta aika ga Manajan Darakta na AEDC waɗanda Opaluwa Eleojo Simeon (Mataimakin Babban Sakataren NUEE, sashin hulɗa da jama’a) da Rosemary Odeh (Mataimakiyar Babban Sakataren SSAEAC, Sashen Yaɗa Labarai) suka sanyawa hannu, sun bayyana cewa sanarwar yajin aikin da suka bayar, na nufin jan hankalin hukumar kamfanin cewa yajin aikin na iya farawa a kowane lokaci, in har aka gaza biyan buƙatun su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here