Rundunar Civil Defence zata baza jami’ai sama da 3000 a Kano yayin bukukuwan babbar Sallah

0
97

Rundunar tsaron a’lumma ta farin kaya Civil Defence (NSCDC) reshen Kano, ta kammala dukkan shirye-shiryen samar da tsaro domin tabbatar da gudanar da bikin Babbar Sallah (Eid-el-Kabir) cikin kwanciyar hankali a faɗin jihar.

Rundunar tayi wannan shiri karkashin jagorancin kwamandan ta na  jiha, Shafi’u Abdulmumini, inda aka amince da tura jami’ai sama da 3,100 don kula da harkokin a’lumma da basu tsaro yayin bukukuwan.

Za a baza jami’an ne a manyan wuraren taro da ibada na Sallah, cibiyoyin shakatawa, kasuwanni da sauran muhimman wuraren jama’a domin samar da tsaro.

A matsayinta na hukumar da ke da alhakin kare muhimman kadarorin gwamnati da tsare rayuka da dukiyoyi, NSCDC ta mai da hankali wajen tabbatar da cewa komai ya gudana cikin aminci a lokacin bukukuwan.

Kwamandan rundunar ya gargaɗi masu tada fitina da su guji aikata laifi, yana mai cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa wajen ɗaukar matakin doka a kan duk wanda aka samu da laifi.

Ya kuma roƙi al’umma su bawa jami’an tsaro haɗin kai domin gudanar da bikin Sallah cikin zaman lafiya da farin ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here