Matsanancin cunkoson ababen hawa ya rutsa da matafiya a hanyar Abuja zuwa Kaduna

0
94

Masu amfani da hanya na fuskantar cunkoson ababen hawa mai tsanani a yankin Bishini da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

A halin yanzu, zirga-zirga ta tsaya cak, inda motocin haya da na masu zaman kansu suka tsaya ba tare da motsi ba.

Alamu na nuna cewa lamarin zai kara tsananta, musamman ga masu tafiya zuwa jihohin Arewa.

Wasu daga cikin fasinjoji da suka makale a hanya na tambayar dalilin da yasa wannan matsala ke faruwa a kowace shekara a tsakanin garuruwan Jere da Katari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here