Kotun Majistare ta 20 da ke Noman’s Land Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Fauziyya Isa Sheshe, ta tura mutane 29 gidan yari bisa zargin su da hannu a kisan CSP Baba Ali, Baturen ‘yan sanda na Rano.
Lauyar gwamnati, Barista Saima Garba, ta karanta tuhumomin da suka haɗa da, hada baki don tayar da tarzoma
Kona gidaje
Shiga gida ba tare da izini ba
Sata
Daga cikin waɗanda ake zargi akwai, Yusuf Baba, Bala Muhammad, Abdullahi Salisu Kere, Dadi Buhari, Musa Munkaila, da Ladi Ismail, wadda ake zargi da tunzura matasa har suka kona gidajen jama’a a Rano.
Kotun ta ɗage sauraren shari’ar zuwa ranar 16 ga Yuni, 2025, yayin da ake ci gaba da bincike.
Rahotanni sun nuna cewa ana neman wasu mutane 20 da suka tsere, dangane da wannan lamari.
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ce ta gurfanar dasu bayan kisan jami’in nata.