An samu bindiga a gidan wanda ake zargi da kisan DPO a Rano–Yan sandan Kano

0
70

Sabbin bayanai sun fito dangane da binciken kisan DPO na Rano CSP Baba Ali, inda rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da gano bindigar AK-47 a gidan wani da ake zargi da hannu cikin lamarin.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an gano bindigar ne yayin bincike a gidan wanda ake zargin.

Kiyawa yace harin ya biyo bayan mutuwar wani matukin babur, Abdullahi Musa, wanda aka kama bisa zargin tuki cikin maye. An tsare shi a ranar Asabar, 25 ga Mayu, 2025, kuma daga bisani ya kamu da rashin lafiya a hannun ‘yan sanda, inda aka kai shi asibitin Rano, amma ya rasu washe gari.

Mutuwar matukin babur ɗin ce ta haifar da tarzoma inda aka kai hari ofishin ‘yan sanda na Rano, aka ƙona wasu sassan ginin ofishin da motoci, tare da jikkata CSP Baba Ali, a harin, kuma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano.

Rundunar ‘yan sanda ta kama mutane 41 da ake zargi da hannu a tarzomar, ciki har da wanda ake zargi da kai farmakin da ya kashe DPO.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce za su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, kuma za su tabbatar da cewa dukan wadanda ke da hannu sun fuskanci hukunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here