Tsohon shugaban EFCC Abdurrashid Bawa zai ƙaddamar da littafi akan badaƙalar man fetur

0
59

Tsohon shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya fitar da sabon littafin da zai ƙaddamar wanda zai fallasa yadda aka yi aringizon kuɗi a tsarin tallafin man fetur a Najeriya.

Bawa, zai ƙaddamar da littafin a ranar 5 ga watan Yuni wanda aka sakawa sunan “The Shadow of Loot and Losses”.

A cewar Bawa, littafin ya bayyana dabarun da aka yi amfani da su wajen wawure biliyoyin naira, da sunan shigo da mai na bogi, maimaita karɓar kuɗi daga gwamnati, da karkatar da mai zuwa ƙetare.

Ya ce littafin ba wai tarihin badakalar fetur zai bayyana kaɗai ba, sai dai zai zama wani kira ne zuwa ga gaskiya da ingantaccen tsarin tafiyar da kuɗin gwamnati.

Bawa ya kasance shugaban EFCC daga 2021 zuwa 2023, kuma ya jagoranci binciken badakalar tallafin mai na 2012.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here