Sojoji sun kashe manyan mayaƙan ISWAP a jihar Borno

0
48

Rahotanni daga jihar Borno sun bayyana cewa dakarun sojin ƙasar nan sun kashe wasu manyan kwamandojin kungiyar ISWAP, Ya Muhammad da Abou Dawuda, a wani samame da suka kaiwa maɓoyar su a ƙaramar hukumar Damboa.

Mai Sharhi akan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ruwaito cewa an hallaka ‘yan ta’addan yayin wani hari da aka kai kwanan nan a garin Damboa.

Dakarun sojin sama ne ne suka kashe mayaƙan ta hanyar jefa musu abubuwa masu fashewa.

Ya Muhammad, wanda aka fi sani da Ameer Fiya na Garno, yana daga cikin manyan kwamandojin ISWAP guda biyar da suka jagoranci kai hare hare masu yawa. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here