Sarkin Kano, na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, ya dakatar da gudanar da bikin hawa na Sallah Babba saboda sha’anin tsaro.
Malam Awaisu Abbas Sanusi, ya fitar, an yanke wannan hukunci bayan tattaunawa da hukumomin tsaro da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki.
Sanarwar tace, rahotannin sirri sun nuna yiwuwar barazanar tashin hankali daga wasu mutane a yayin bukukuwan Sallah, wanda hakan ya sa masarautar ta dauki matakin kare lafiyar al’umma.
Dakatarwar ta zo kamar yadda aka yi a lokacin bikin sallah ƙarama, data gabata, inda aka hana gudanar da hawan dawakai domin kauce wa rikice-rikicen da ka iya tasowa.
Sanarwar ta kuma yi kira ga al’ummar Kano da su kara zage damtse wajen addu’o’in neman zaman lafiya mai dorewa a Kano da Najeriya baki ɗaya.