Majalisar dokokin Jihar Nasarawa ta bukaci hukumomi su gaggauta bincike tare da daukar mataki kan kisan CSP Muhammad Ali, DPO na Rano a Jihar Kano, wanda aka kashe bayan zargin azabtar da wani matashi.
Majalisar ta bayyana kisan a matsayin take doka, tare da jajanta wa iyalan mamacin da Rundunar ‘Yan Sanda.
Majalisar ta kuma nemi a gudanar da bincike na gaskiya da adalci, tare da daukar matakan kare jami’an tsaro da sa ido kan aikinsu.
Majalisar ta jaddada cewa akwai bukatar adalci da daukar mataki a kan duka bangarorin da abin ya shafa.