Akalla mutune bakwai ne suka mutu sakamakon kifewar wani kwale-kwale a ƙaramar hukumar Shagari da ke jihar Sokoto.
Lamarin ya faru da safiyar Litinin, da misalin ƙarfe 9:30, a lokacin da matafiya ke kan hanyarsu daga Gidan Hussaini zuwa ƙauyen Gwargawu, kamar yadda hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta tabbatar.
Rahoton hukumar ya bayyana cewa kifewar jirgin ruwan ta faru sakamakon iska mai ƙarfi da ta mamaye yankin a lokacin da lamarin ya faru.
Wannan na zuwa ne kasa da shekara guda bayan wasu manyan hadurran jirgin suka faru a wasu sassan ƙasar nan.
Idan za’a iya tunawa ko a watan Oktoban 2024, wani jirgin ruwa ya kife da kusan fasinjoji 300 a yankin Mokwa da ke jihar Neja.
Haka zalika, a watan Satumban 2023, mutum 24 sun mutu a wani hatsarin jirgin ruwa a jihar Neja.
Masana na ci gaba da bayyana damuwarsu kan yawan kifewar jiragen ruwa a Najeriya, musamman a sassan da ruwa ke zama hanya ta yau da kullum ga al’umma.