Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sakin naira biliyan 2 daga asusun gwamnatin tarayya don sake gina gidajen da ambaliya ta lalata a Mokwa, dake Jihar Neja.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya sanar da hakan yayin ziyararsa zuwa yankin, inda ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa ya kuma bada umarnin tura manyan motoci 20 ɗauke da shinkafa don rabawa ga waɗanda abin ya shafa.
Shettima ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu na tare da al’ummar Mokwa, tare da alkawarin gyara gadojin da ambaliyar ta rushe.
Fiye da mutane 200 ne aka ce sun mutu sakamakon ambaliyar da ta auku a ranar 28 ga Mayu, 2025.