Gurɓatar iska ya fara illata lafiyar al’ummar wasu unguwannin Kano

0
52

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana damuwa kan gurɓatar iska a wasu yankunan birnin Kano irin su Gaida, Ja’en, Sabon Titi da Kasuwar Sharada.

Rahoton Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ya nuna cewa wadannan yankuna na fama da gurbacewar iska mai barazana ga lafiyar ɗan Adam.

Kwamishinan Muhalli, Dr. Dahir Hashim, ya ce akwai bukatar kowa ya bayar da hadin gwiwar wajen kare muhalli.

Wasu mazaunan wadannan unguwanni da aka bayyana sun bayyana fuskantar matsalolin lafiya da suka ƙunshi tari da sauran matsalolin numfashi.

Wani rahoto daga dandalin IQAir ya nuna cewa matakin gurɓacewar iska a yankunan ya kai AQI 79, inda ƙwayoyin ƙura masu shiga jiki ke zama babban barazana.

Masana lafiya sun ja hankalin jama’a da su rage fita waje, su rika amfani da takunkumin fuska, kuma su nemi mafita daga guraren da ke da mummunar iska, yayin da gwamnati na shirye-shiryen ɗaukar matakan shawo kan matsalolin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here