Ganduje na gudanar da aikin Hajji a lokacin da yake ƙara samun karɓuwa ta fuskar siyasa

0
38

 Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, na daga cikin dubban ‘yan Najeriya da ke gudanar da aikin Hajji a ƙasar Saudiyya.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano na wa’adin mulki biyu, kuma gogaggen ɗan siyasa, zuwansa birnin Makkah domin wannan muhimmin aikin ibada na Musulunci ya haifar masa da karɓuwa sosai daga mabiyansa da al’ummar Musulmai gaba ɗaya.

Duk da kasancewar yayi nesa da gida, tasirin Dr. Ganduje na ci gaba da yin ƙarfi a gida Najeriya. 

A karkashin jagorancinsa, jam’iyyar APC ta kara samun karfi, inda manyan ‘yan siyasa ke sauya sheƙa zuwa jam’iyyar tare da karɓuwa daga sassa daban-daban. 

Masana harkokin siyasa na danganta wannan nasara da salon jagoranci na haɗin kai da hikimar siyasa da Ganduje ke da ita.

A ‘yan makonnin da suka gabata, Dr. Ganduje ya samu yabo sakamakon yadda ya nuna tausayawa bayan hatsarin da ya rutsa da wasu matasa ‘yan wasa daga Kano. Ya shiga sahun sauran shugabannin Arewa wajen nuna alhini da kiran a gudanar da bincike mai zurfi. Sakon ta’aziyyarsa da addu’o’in da ya aiko sun nuna yadda yake jin zafin abin da ya faru ga jama’ar daya fito daga cikin ta.

Tun bayan da ya karɓi ragamar shugabancin jam’iyyar APC, Dr. Ganduje ya mayar da hankali wajen gyara jam’iyyar, yana ƙarfafa hadin kai da kishin kasa. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here