Sarkin Kano Muhammad Sunusi ya umarci hakimai su fito hawan Sallah

0
66

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya umarci dukkan Hakimai da ‘yan majalisar masarautar da su hallara a birnin Kano domin yin shirin hawan babbar Sallah mai zuwa.

Sanarwar da Sakataren Majalisar Masarautar, Alhaji Abba Yusuf Danmakwayon Kano, ya fitar ta bayyana cewa Hakiman za su iso Kano da dawakan su a ranar Laraba, 4 ga Yuni, 2025.

Za su kai gaisuwa ga Sarkin Kano a ranar Alhamis, 5 ga Yuni, kafin a gudanar da wani taro na musamman domin tsara yadda hawan Sallah zai kasance.

Majalisar ta ce an tuntubi shugabannin kananan hukumomi domin sauƙaƙa musu hanya, tare da roƙon Allah ya sa bikin ya gudana lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here