Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta da haramta duk wani taron hawan Sallah a lokacin bikin babbar Sallah, saboda dalilan tsaro.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne bayan samun rahotannin sirri da suka nuna barazanar amfani da hawan Sallah wajen tayar da hankali da tada tarzoma.
Ya ce wannan matakin an fara ɗaukar sa tun lokacin sallah ƙarama.
Har ila yau, rundunar ta bayyana wasu ƙa’idoji da za a bi domin tabbatar da zaman lafiya a lokacin bikin, ciki har da:
Haramta hawa dabbobi ko dawaki,
Hana tseren motoci ko tuƙin ganganci,
Haramta ɗaukar makamai ba bisa ƙa’ida ba,
Hana ɗaukar abubuwan da za su iya tayar da hankali.
An kuma ja kunnen iyaye da su kula da ‘ya’yansu kada su bari su shiga cikin shirin bata gari.
Daga ƙarshe, rundunar ta bukaci a ci gaba da yin addu’a ga jihar Kano, ƙasa, da kuma ‘yan wasan Kano da suka rasa rayukansu yayin dawowa daga gasar National Sports Festival.