Har kuka nake yi in na tuna da cin amanar da Fubara yayi min—Wike

0
101

Ministan birnin tarayya Abuja  Nyesom Wike, ya ce yana jin ƙunci da ƙwalla a duk lokacin da ya tuna da cin amanar da dakataccen gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara ya yi masa.

A wata hira da ya yi da manema labarai a ranar Litinin, Wike ya bayyana cewa Fubara yana goyon bayan waɗanda ke ƙoƙarin yaƙar sa, amma ba su da ƙarfin yin hakan.

Wike ya ce Fubara ya ci amanarsa ta hanyar haɗin gwiwa da masu burin ganin yayi rashin nasara a harkokin siyasa, duk da cewa shi ne ya taka rawa wajen tabbatar da nasarar Fubara a matsayin gwamnan Jihar Rivers.

Ya ƙara da cewa mafita daga rikicin siyasar da ke faruwa a Jihar Rivers yana hannun Fubara, yana mai cewa ya shirya domin sasanci muddin gwamnan da aka dakatar na da niyyar Kawo zaman lafiya.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here