Hafsan hafsoshin tsaron ƙasa ya koma Benue da zama sakamakon rashin tsaro

0
100

Hafsan hafsoshin tsaron ƙasa Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya sauka a birnin Makurdi, na jihar Benue, sakamakon hare-haren da kungiyoyin ‘yan bindiga ke kaiwa al’umma, wanda ke ci gaba da janyo hasarar rayuka da dukiyoyi.

Rahotanni sun nuna cewa kashe-kashen da suka zama tamkar ruwan dare a jihar, sun yi sanadin mutuwar mutane da dama, da jikkata wasu da dama, tare da kona gidaje da dama tare da lalata muhallin mutane da dama.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Laftanar Janar Oluyede ya bar Abuja da safiyar Talata tare da manyan jami’an rundunar soji daga hedikwatar sojin kasa domin duba halin da ake ciki a jihar don kawo mafita.

Majiyoyi sun bayyana cewa shugaban sojin ya bayar da umarnin tura karin dakarun soja zuwa jihar Benue domin fatattakar ‘yan ta’adda da ke addabar al’umma.

Har ila yau, Olufemi zai gudanar da muhimman taruka da dukkan kwamandojin rundunoni dake Benue domin tattaunawa kan yadda za a kawo karshen wannan matsala, da kuma nazarin nasarorin da aka samu a ayyukan da ake gudanarwa a halin yanzu.

Idan za’a iya tunawa dai hare haren da aka fuskanta a jihar Benue a baya bayan nan yayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 60.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here